Shugaban Guinea Bissau zai rushe gwamnati | Labarai | DW | 14.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Guinea Bissau zai rushe gwamnati

An dai shiga rudani na 'yan siyasa a kasar tun a shekarar bara, kokarin shawo kan matsalolin kuma sun gagara.

Shugaban kasar Guinea Bissau Jose Mario Vaz ya bayyana a ranar Litinin din nan cewa zai rushe gwamnatin Firaminista  Baciro Dja dan samun dama ta nada wani na daban, nan ba da dadewa ba, abin da ya ke ganin zai taimaka wajen kawo karshen kiki-kaka na siyasar kasar da aka shiga sama da shekara guda.

Dja dai an nada shi ne a watan Mayu da zummar ya samar da gyara a fannin harkokin siyasar kasar da ya tabarbare tun a watan Agusta na shekarar 2015, sai dai ya gaza wajen samun goyon baya na baki dayan mambobin jam'iyyar PAIGC da ke mulki.