1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Gambiya ya yi afuwa ga fursunonin siyasa

Suleiman BabayoJuly 22, 2015

Wadanda aka tuhuma da yunkurin kifar da gwamnati Gambiya a watan Disamba ba za su ci gajiyar shirin wannan ahuwa ba

https://p.dw.com/p/1G3NS
Yahya Jammeh 2006
Hoto: picture-alliance/AP/Rebecca Blackwell

Shugaba Yahya Jammeh na kasar Gambiya ya saki daukacin fursunoni da aka tuhuma da cin amanar kasa daga shekarar 1994 zuwa shekara ta 2013, albarkacin bikin cika shekaru 21 da kwace madafun ikon kasar cikin juyin mulki.

Sai afuwar ta shugaban ba ta shafi wadanda aka kama a watan Disamban da ya gabata ba, ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin kasar da ke yankin yammacin Afirka. Shugaba Jammeh dan shekaru 50 da haihuwa ya kwace mulki daga hannun Shugaba Dauda Jawaba, wanda ya jagoranci kasar ta samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya. Kungiyoyin kare hakkin dan Adam suna zargi gwamnatin kasar ta Gambiya da musguna wa mutane.