1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Gabashin Timor ya kafa dokar ta ɓaci.

May 31, 2006
https://p.dw.com/p/Buw4

Shugaba Xanana Gusamo na gabashin Timor, ya kafa dokar ta ɓaci, tare da kuma karɓar shugabancin rundunar sojin ƙasar. Hakan dai ya biyo bayan tahse-tashen hankullan dac suka ɓarke ne a Dili, babban birnin ƙasar. A halin da ake ciki dai, shugaban ya ƙi amsa kiran da ’yan adawa ke yi na ya sallami Firamiya Mari Alkatiri daga muƙaminsa.

Tun cikin watan jiya ne dai rikici ya ɓarke a ƙasar, yayin da Firamiyan ya sallami kusan kashi 40 cikin ɗari na sojojin ƙasar daga gun aikinsu. Kusan mutane 20 ne rahotanni suka ce sun rasa rayukansu a rikicin. A halin yanzu dai, dakarun ƙasa da ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Austreliya ne ke sintiri a babban birnin na Dili, inda suke ƙoƙarin kwantad da tarzomar da ta ɓarke tsakanin gungun ’yan ƙasar masu hamayya da juna.