1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Faransa yayi Allah wadan harin Bus a Merseille

October 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bu54

Shugaba Jacques Chirac na kasar Faransa ,yayi Allah wadan hari da wasu yan ta kife suka afkawa wata bus da dashi a birnin Marseille dake kudancin kasar,harin daya bar wata mace cikin hali na m,atsanancin jinya sakamakon konewa datayi.Harin wanda ya auku a jiya asabar ya haifar da rudanin yiwuwar sake barkewar rikici a wannan kasa,adaidai lokacin da ake cika shekara guda da barkewar rigingimu a ungunanin baki,a kasar ta faransa.Sanarwar data fito daga fadar Shugaba Chirac na nuni dacewa,gwamnati zata dauki dukkan matakan da suka dace na gano wadanda keda hannu a wannan harin daya bayyana da kasancewa abun takaici.Bugu da kari Premiyan Faransa Dominiquie De Villepine,yace zai jagoranci taro na musamman a gobe,adangane da daukan matakan samar da tsaro a dukkan harkokin sufurin jamaar a wannan kasa.Kazalikqa ministan harkokin cikin gida Nicholas Sarkozy ,ya sanar da tura karin jamian yansanda zuwa birnin na merseille,domin tabbatar da tsaro.