Shugaban Faransa yace ba zai sake tsayawa takara ba | Labarai | DW | 12.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Faransa yace ba zai sake tsayawa takara ba

Shugaban kasar Faransa Jacque Chirac yace ba zai sake tsayawa takara a zaben wata mai zuwa bayan shekaru 45 na harkokin siyasarsa,yana mai kira ga Faransawa da suyi warsi da tsatsauran raayi.

Chirac dan shekaru 74 yayi alkawarin ci gaba da bada gudumowarsa tare da bautawa kasarsa har iyaka rayuwarsu.

Shugaban na Faransa wanda ya dare karagar mulki tun a 1995 yace ba zai baiyana wanda yake goyawa baya ba tukuna cikin yan takarar kujerar shugaban kasa sai dai kuma yayi kira ga yan kasar da kada su zabi mai tastausarn raayi,mai nuna bambanci ko kyamar jinsi,yana mai baiyana fatar masu jefa kuriar zasuyi watsi da Jean Marie Le Pen wanda ya zo na 2 a zabern shugaban kasa na 2002.