Shugaban Faransa Sarkozy ya naɗa sabuwar gwamnati | Labarai | DW | 18.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Faransa Sarkozy ya naɗa sabuwar gwamnati

Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ya naɗa yan majalisar gudanarwar gwamnatin sa. Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Francois Fillon a matsayin P/M, sai kuma Bernard Kouchner wanda ya sami matsayin Ministan harkokin waje. Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Tsohon P/M Alain Juppe wanda aka baiwa Ministan muhalli da kuma Jean-Louis Borloo a matsayin Ministan ƙwadago da tattalin arziki.