1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Faransa na ziyara a Amirka

Yusuf Bala Nayaya
April 23, 2018

Shugaba Donald Trump na Amirka ya tarbi takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a fadar White House a wannan rana ta Litinin inda zai fara ziyarar aiki ta kwanaki uku.

https://p.dw.com/p/2wU7b
Frankreich Nationalfeiertag in Paris | Trump & Macron
Ana dai ganin alamu na fahimta tsakanin Trump da MacronHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Euler

A lokacin wannan ziyara dai ana sa rai ta mayar da hankali kan batun da ya shafi harkokin kasuwanci da Shugaba Macron ya ce zai karfafi gwiwar Amirka kan batun kasuwanci cikin hadaka. Har ila yau Shugaba Macron ya ce za su kuma duba batun takkadamar da ke tsakanin kasar Amirka da sauran kasashen Yamma kan shirin makamin nukiliya na Iran.

A ranar Talata ne dai za a tattauna muhimmann batutuwa tsakanin shugabannin a fadar ta White House inda a nan ne ma dai za su yi taron manema labarai. A ranar Laraba kuwa Macron zai yi jawabi a gaban hadin gwiwar majalisun kasar, abin da ke zuwa a yayin da ake tuni da ranar 25 ga watan Afrilu na shekarar 1960 lokacin da Charles de Gaulle tsohon shugaban Faransa ya yi irin wannan jawabi a gaban hadin gwiwar majalisun na Amirka.