1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas zai kira zabe na gaban wa´adi

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya ce zai kira sabon zabe shugaban kasa da na ´yan majalisun dokoki na gaba da wa´adi. Shugaban ya yanke wannan shawara ce sakamakon rushewar tattaunawar da ake yi na kafa gwamnatin hadin kan kasa tsakanin kungiyar Hamas da kungiyar Fatah ta shugaban na Falasdinawa a makon da ya gabata. Nan take kuwa jami´an Hamas sun yi tir da wannan shawara inda suka yi ikirarin cewa Abbas bai da ikon kiran sabon zabe.