Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ya ce nan ba da daɗewa ba za a sako sojan Isra’ilan nan da ’yan ƙungiyar Hamas suka cafke. | Labarai | DW | 28.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ya ce nan ba da daɗewa ba za a sako sojan Isra’ilan nan da ’yan ƙungiyar Hamas suka cafke.

Shugaban Hukumar Falasɗinu, Mahmoud Abbas, ya faɗa wa maneman labarai cewa, ya yi imanin na ba da daɗewa ba, za a sako sojan Isra’ilan nan da ’yan Jungiyar Hamas suka cafke a kan iyakar zirin Gaza da ƙasar bani Yahudun a watan jiya. Abbas ya bayyana hakan ne ne a birnin Rom, bayan ganawar da ya yi da Firamiyan Italiya Romano Prodi. Da yake amsa tambayoyin maneman labaran, Abbas ya ce ana nan ana ta ƙoƙarin cim ma sako kamammen sojan. Amma reshen soji na ƙungiyar Hamas ɗin, wanda ke garkuwa da sojan, ya yi watsi da jawabin da shugaban Falasɗiwanan ya yi. Wani kakakin reshen ya ce, Abbas ba shi da ikon yanke shawarar sako sojan