Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, ya bai wa Ƙungiyar Hamas wa’adin sa’o’i 48 da ta yi amanna da wata ƙasidar da ya gabatar kan Isra’ila. | Labarai | DW | 07.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, ya bai wa Ƙungiyar Hamas wa’adin sa’o’i 48 da ta yi amanna da wata ƙasidar da ya gabatar kan Isra’ila.

A gwagwarmayar da ƙungiyoyin Falasɗinawa na Fatah da Hamas ke yi kan madafan iko, shugaban Falasɗinawan Mahmoud Abbas, ya tsawaita wa’adin da ya bai wa ƙungiyar Hamas da sa’o’i 48, na ta amince da wata ƙasidar da ya gabatar, wadda ke nufin yarjewa da wanzuwar Isra’ila tamkar ƙasa mai cin gashin kanta. Shi dai Abbas, ya yi barazanar kiran zaɓen raba gardama, idan Hamas ɗin ta yi watsi da wannan ƙasidar. Sakamakon binciken ra’ayin jama’a da aka gudanar dai na nuna cewa, mafi yawan Falasɗinawan na goyon bayan shawarar ta Mahmoud Abbas, wadda ta tanadi kafa ƙasar Falasɗinu da ta ƙunshi duk yankunan Gaɓar Yamma da Zirin Gaza, wato yankunan da Isra’ila ta kame daga hannun Masar da Jordan, a cikin yaƙin 1967.

A wani labarin kuma, wata kakakin rundunar sojin Isra’ilan ta tabbatad da rahotannin cewa, jiragen saman yaƙin ƙasar, sun ragargaza wani Gini a Zirin Gaza, wanda ’yan ta kifen Falasɗinawa ke amfani da shi wajen shirya hare-harensu a kan ƙasar bani Yahudun. Rahotanni sun ce kafin harin jiragen saman dai, sai da ’yan ta kifen Falasɗinawa suka harba rokoki guda 9 cikin Isra’ila, inda suka ji wa wata mace ɗaya rauni.