Shugaban Brazil Lula da Sailva ya yi kira da a cika burin yarjejeniyar Kyoto | Labarai | DW | 26.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Brazil Lula da Sailva ya yi kira da a cika burin yarjejeniyar Kyoto

Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya yi kira ga kasashe masu arzikin masana´antu da su cika ka´idojin yarjejeniyar birnin Kyoto akan kare muhalli. Shugaban na Brazil ya fadawa babban taron MDD a New York cewa dole a hada karfi waje guda don cimma burin da aka sa gaba musamman bayan cikar wa´adin yarjejeniyar ta Kyoto. Da Silva ya ce: “Muna bukatar daukar nagartattun matakai bayan shekara ta 2012. Dole mu kara mayar da himma don ganin kasashe da yawa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar. Ya zama wajibi su ma kasashe masu tasowa su shiga cikin yaki da sauyin yanayi. Kowace kasa na da alhakin da ya rataya wuyanta na kare al´mominta.”

Yarjejeniyar kyoto ba ta dorawa Brazil a matsayin kasa mai tasowa wani nauyi na musamman ba. To amma a baya Amirka ta yi ta matsa lamba don ganin kasashe masu samun matsakaicin ci-gaban masana´antu kamar China da Brazil sun dauki matakan rage fid da hayaki mai gurbata yanayi.