1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar kama masu masana'antu a Banizuwela

Yusuf BalaMay 15, 2016

'Yan adawar dai sun tattara sa hannu na mutanen kasar miliyan daya da dubu dari takwas wadanda ke son shugaban ya sauka.

https://p.dw.com/p/1Io6s
Venezuela Präsident Nicolas Maduro
Shugaba Nicolas MaduroHoto: Imago/Xinhua

Shugaban kasar Banizuwela Nicolas Maduro ya yi gargadi a yammacin ranar Asabar cewar, zai kwace duk wata masana'anta da ta tsaida gudanar da aikinta ya ba wa al'umma, sannan a shirye yake ya sanya shugabannin masana'antun da suka ki bin wannan umarni a gidan kaso.

Masu adawa da gwamnatin shugaba Maduro dai sun hau kan titunan kasar inda suke kokawa da ci gaban matsi na tattalin arziki, yayin da abinci da makamashi da magunguna ke takaita a kasar tun daga watan Janairu.

'Yan adawar dai sun tattara sa hannu na mutanen kasar miliyan daya da dubu dari takwas wadanda ke bukatar ganin an kada kuri'ar raba gardama da za ta yi awon gaba da shugabancin na Maduro, sai dai hukumar da ke tsara zabe a kasar ta Banizuwela a ranar Juma'a ta gaza amincewa da bukatarsu.

Su kuwa masu masana'antu na kokawa da rashin kudade ne da za su yi amfani da su dan siyen kayayyaki da suke sarrafawa, abin da shugaban ya ce korafi ne mara tushe. Sannan barazanarsu ta rufe masana'antu kaddamar da yaki ne kan tattalin arzikin kasa.