Shugaban AU ya shawarci aika runduna a iyakokin Tchad da RCA
November 15, 2006Shugaban ƙasar Congo Brazaville, bugu da ƙari shugaban ƙungiyar tarayya Afrika, Denis Sassou Nguesso ya shawarci aika runduna a iyakokin ƙasashen Tchad, da Jamhuriya Afrika ta tsakiya, wadda zata sa ido, ga tabarbarewa mattakan tsaro.
Rikicin da ke gudana a yankin Darfur na ƙasar Sudan, ya harbi wannan ƙasashe, ta hanyar rigingimmun tawaye, da na ƙabilanci, babu ƙaƙƙabtawa.
Hukumomin N´Djamena da Bangui, sun issar da kira, ga MDD, da ƙasar France, sun kai masu ɗauki cikin gagawa,domin magance wannan matsala, da ke matsayin barazana ga zaman lahia a yankin baki ɗaya.
A ɗaya wajen Denis Sassun Nguesso, ya yi kira ga shugaba El Beshir ya amince da karbar rundunar shiga tsakani ta MDD, a yankin Darfur, wadda ko shaka babu, zata taimaka, wajen shawo kann wannan rikici.