Shugaban Angola ya sake dage zaben kasar | Labarai | DW | 27.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Angola ya sake dage zaben kasar

Shugaban kasar Angola,Jose Eduardo Dos Santos,ya sanar da sake dage zaben kasar karo na farko tun bayan yakin basasar kasar,wadda aka shirya zaa gudanar cikin wannan shekara zuwa shekara mai zuwa.

Yace zaben ba zai gudana ba har sai an gyara hanyoyin mota dana jiragen kasa na kasar baki daya.

Yace jamiyarsa zata ga cewa gwamnati ta gyara wadannan hanyoyi domin baiwa jamaa damar zirga zirga cikin walwala a lokacin zaben.

A dai karshen watan disamba ne shugaba dos santos yace ba zai saka ranar zabe ba har sai an kammal rajistar masu jefa kuria wanda zai samu amincewar majalisar jamiyun siyasun kasar.

Jamiyar dos santos take mulkin Angola tun lokacinda kasar samu yancin kanta a 1975.

A 1992 anyi zabe a kasar wanda jamiyar UNITA tace an tafka magudi a cikinsa,kafin sake barkewar yakin basasa shekaru 10 baya.