Shugaban Amurka ya sanarda kai ziyara Afurka a 2008 | Labarai | DW | 30.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Amurka ya sanarda kai ziyara Afurka a 2008

Shugaban Amurka George Bush ya sanar da cewa shi da uwargidansa Laura Bush zasu kai ziyara ƙasashen Afrika da ke kusa da sahara a farkon shekara ta 2008,shekara ta ƙarshe a mulkinsa.Cikin wani jawabi da ya yi don tunawa da ranar yaƙi da cutar AIDS ta duniya shugaban na Amurka ya ce Amurka ta bada fifiko kan sabuwar danganta da ta ƙulla da nahiyar Afrika.Bush ya kuma baiyana irin taimako da Amurka take bayarwa ga yaƙi da cututtukan AIDS da Malaria a Afrika.Bush wanda bai baiyana sunayen ƙasashe da zasu kai ziyarar ba,ya ce yana fatar ganin sakamakon irin taimako da Amurka ta ke bayarwa,ya kuma nunawa kasashen Afrika cewa Amurka abokiyar huldarsu ce da zasu iya dogara da ita.