1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Amurka ya lashi takobin samun nasa a Gabas ta Tsakiya kafin ya bar mulki

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta ce shugaban Amurka George Bush ya ƙuduri aniyar samun nasara tsakanin Israila da Palasɗinwa kafin ya bar ofis.Ta ce muddin dai taron mako mai zuwa na samarda zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ya samu nasara da ake bukata,masu shiga tsakani na Israila da Palasɗinwa zasu iya cimma yarjejeniya ta samarda ƙasashe biyu masu maƙwabtaka da juna.Gwamnatin Amurka dai tuni ta aike da takardun gaiyata ga ƙasashe da ƙungiyoyi 40.Taron na kwana guda a Annapolis ƙasar Amurka shine na farko irinsa kan zaman lafiya na Gabas ta Tsakiya tun shekara ta 2000.