Shugaban Amurka ya baiyana imanin samun nasara a taron yankin Gabas ta Tsakiya | Labarai | DW | 26.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Amurka ya baiyana imanin samun nasara a taron yankin Gabas ta Tsakiya

Shugaban Amurka George Bush ya baiyana imaninsa game da nasara taron zaman lafiya na yankin Gabas ta Tsakiya wadda za a fara gobe talata a ƙasar Amurka.Kusan kasashe 50 ne ake sa ran zasu halarci taron cikinsu kuwa da Syria da kuma Saudiya.Tuni dai shugabannin ɓangarorin da abin ya shafa suka isa birnin Washington inda a yau Bush ya gana da firaministan Israila Ehud Olmert a fadar gwamnati.

Nan gaba Bush zai gana da Mahmud Abbas.Taron shine irinsa na farko na farfaɗo da shirin zaman lafiya na Gabas ta Tsakiya cikin shekaru 7 ana kuma sa ran zai aza tubalin samarda ƙasar Palasdinu.