Shugaban Amurka ya alkawarta aikewa da abinci zuwa Darfur | Labarai | DW | 08.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Amurka ya alkawarta aikewa da abinci zuwa Darfur

Shugaba Bush na Amurka yace ya bada umurnin a aike da abinci na agajin gaggawa zuwa kasar Sudan,domin taimakawa jamaa da dama da suka shiga halin kaka nikayi,ya kuma yi kira ga majalisar dokokin Amurkan data amince,da dala miliyan 225 domin sayen abinci ga jamaar darfur.

Bush yace ya bada umurnin ayiwa manyan jiragen ruwa 5 na Amurka lodin kayaiyakin abinci zuwa Sudan,ya kuma bada umurnin a sayen karin ton 40,000 na abinci zuwa Sudan din.

Hakazalika Bush yace,sakatariyar harkokin wajen Amurka Codoleeza Rice,zata yi jawabi a gaban komitin sulhu na majalisar dinkin duniya a gobe talata idan Allah ya kai mu,inda zata bukaci a bullo da wani kudiri na majalisar dinkin duniya wanda zai gaggauta aikewa da dakarun majalisar zuwa Darfur.