Shugaban Amirka George Bush a Abu Dhabi. | Labarai | DW | 13.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Amirka George Bush a Abu Dhabi.

Shugaban Amirka George W. Bush ya yi kira ga ƙawayen Amirka na yankin Gulf, da su tashi tsaye wajen tinkarar matsalar da ake fuskanta da Iran. A lokacin da ya ke jawabi a birnin Abu Dhabi, shugaba Bush ya soki lamirin shugabannin Iran.

Bush ya ce Iran tana tursasawa makwabtanta da makamai masu linzami, tare da yin watsi da ƙudurorin kwamitin sulhu na Majalisar ɗinkin Duniya, kana ta na kuma zaman barazana ga yankin baƙi ɗaya a dangane da muradinta na mallakar makaman nukiliya….

Sugaba Bush ya ƙara da cewar Iran ta kawo cikas a harkokin tsaro na ƙasar Libanon sabili da tallafawa dakarun Hizbola, ya kuma zargi Iran da goyan bayan ƙungiyar Hamas a Iraqi. Bush yana ziyartar Daular Larabawa kann yawon sa na yankin, inda yake fatan shawo kann al’uman Palesdinu da Izraila, don su ratabba hannu kann yarjejeniyar zaman lafiya a yankin kafin karshen wa’adinsa kan mulki wanda zai ƙare nan da shekara ɗaya.