1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Afghanistan ya karyata kafa rundunar sojin sa kai

June 11, 2006
https://p.dw.com/p/BuuU

Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai ya karyata rahotannin dake cewa,yana shirya wata sabuwar rundunar sojin sa kai da zata yaki yan Taliban a kudancin kasar,amma kuma yace zaa taimakwa rundunonin tsaro a yankin da karin sabbin jamiai daga jamaar yankin domin taimaka masu.

Wanna kalami na Karzai yazo ne biyowa bayan sake kunno kai mafi girma da yan Taliban sukayi tun korarsu daga mulki a 2001.

Fiye da mutane 500 suka rasa rayukansu cikin makonni 3 kadai.

Wasu kafofin yada labarai cikin yan makonnin nan sun bada rahoton cewa,gwamnatin Karzai yana duba yiwurar kafa rundunar sojin sa kai na jamaar kauyukan yankin domin su yaki yan kungiyar Taliban .

Mai magana da yawun shugaba Karzai,Karim Rahimi yace jamian da zaa diba a kauyukan zasu kasance tamkar yan sanda ne da zasu taimakawa jamian tsaro na kudancin kasar.