Shugaban adawa na Kenya ya bukaci shugaba Kibaki ya amince ya sha kaye | Labarai | DW | 30.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban adawa na Kenya ya bukaci shugaba Kibaki ya amince ya sha kaye

Shugaban adawa na Kenya Raila Odinga yayi kira ga shugaba Mwai Kibaki da ya amince da kaye da ya sha a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar. Raila Odinga ya zargi shugaba Kibaki da yin maguɗi a zaɓen. Yanzu haka kwanaki uku bayan zaɓen tare kuma da samun tsaiko wajen ƙidaya kuri’u, Odinga yace gwamnati ta rasa dukkan damar da take da ita na ci gaba da mulkin al’umma. Odinga yana kan gaba inda kuri’unsa suka ɗara na shugaba Kibaki da 38,000,cikin kashi 90 cikin 100 na kuri’u da aka ƙirga.