Shugaban ƙasar Kwango Joseph Kabila, ya yi kira ga abokin hamayyarsa Jean-Pierre Bemba da ya jane dakarunsa daga birnin Kinshasa. | Labarai | DW | 23.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban ƙasar Kwango Joseph Kabila, ya yi kira ga abokin hamayyarsa Jean-Pierre Bemba da ya jane dakarunsa daga birnin Kinshasa.

A gwagwarmayar da suke yi na mamaye madafan iko a ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango, rahotanni sun ce shugaban ƙasar Joseph Kabila, ya umarci abokin hamayyarsa Jean-Pierre Bemba da ya janye dakarunsa daga babban birnin ƙasar. A wata fira da ya yi da wakiliyar Deutsche Welle a birnin Kinshasa, kakakin shugaban, Kudura Kasongo, ta tabbatar cewa lalle ne shugaban ya ba da wannan umarnin. Kamar dai yadda ta bayyanar:-

A matsayin shugaban dai, wannan matakin shi kaɗai ne hanyar tabbatad da tsaro. Al’umman ƙasar na bukatar zaman lafiya. Su ko waɗanda suke ta da zaune tsaye, dakarun Bemba ne. Sabili da haka ne nake ganin wannan matakin ya dace, don a kori dakarun daga birnin. Hakan ne zai sa jama’a su iya zama cikin kwanciyar hankali, su kuma iya tafiyad da harkokinsu, yayin da suke jiran baban kotun ƙoli ta ƙasa ta yanke shawararta.“