Shugaban ƙasar Iraqi zai ziyarci Iran a ƙarshen makon nan don tattauna batun shawo kan rikicin da ke addabar ƙasarsa. | Labarai | DW | 21.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban ƙasar Iraqi zai ziyarci Iran a ƙarshen makon nan don tattauna batun shawo kan rikicin da ke addabar ƙasarsa.

Rahotanni daga birnin Bagadaza, sun ce shugaban ƙasar Iraqi, Jalal Talabani ya amsa gayyatar da aka yi masa zuwa birnin Teheran a ƙarshen mako nan don tattauna batun shawo kann rikicin da ke barazanar sanya ƙasarsa cikin yaƙin basasa. Amma wani kakakin shugaban ya ƙaryata rahotannin da ke nuna cewa shugaba Bashar al-Assad na Siriya ma zai shiga shawarwarin. Ita Siriyan da kanta ma ta yi inkarin rahoton. A kwanakin bayan ne dai Birtaniya ta shawarci Amirka da ta amince da shigar Iran da Siriya cikin shawarwarin nemo bakin zaren warware rikicin Iraqin.

A halin da ake ciki a Iraqin dai, rahotanni sun ce har ila yau ana ci gaba da tashe-tashen hankulla. A jiya kawai fiye da mutane 25 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da aka kai a Bagadaza, da Ramadi da Baquba da Kirkuk.