Shugaban ƙasar Guinee-Conakry ya tsige Praminista daga muƙamin sa | Labarai | DW | 05.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban ƙasar Guinee-Conakry ya tsige Praminista daga muƙamin sa

A yammacin jiya ne, shugaban ƙasar Guinee Konacry,Lansana Konte, ya yi gagaramin garambawul ga gwamnatin sa.

A cikin wanan garambawul, ya sallami ministoci 12, sannan ya ƙarffafa muƙamin Praminista, Cellou Dalein Diallo.

Sabuwar dokar da shugaban ya sa hannu a kanta jiya, ta tattara kujerun ministocin kuɗi, da na passali da tattalin arziki, da kuma ministan harakokin waje, ƙarƙashin mulkin Praminista.

Sabin ministoci 13, su ka shigo a cikin gwamnatin.

A nasu ɓangare yan adawa, na bayyana bukatar su, ta girka gwamnatin riƙwan ƙwarya, ta la´akari da yadda, shugaban ƙasa Lansana Konte,ya zama shugaban je ka na yi ka, dalili da matasanciyar rashin lahia, da ya ke fama da ita, a tsawan shekaru da dama.

A wani mataki mai ban mamaki, a na cikin gabatar da sunayen sabin ministocin, sojoji su ka tada bori, a birnin Conakry, inda su ka kai,hari, ga cibiyar gidan redio na kasa, su ka ƙwace takardar ta garambawul.

Jim kaɗan ,bayan haka, fadar shugaban ƙasa ta fido wata sabuwar sanarwa , inda, ta bayana soke wannan garambawul.

Sai kuma a ɗazun nan, kwaram, kamar daga sama, rahotani daga ƙasar su ka bayyana cewar shugaba Lansana Konte, ya tsige Praministan daga muƙamin sa, bayan ya zarge sa da cin amana.