Shugaban ƙasar Guinea ya gana da friministansa | Labarai | DW | 02.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban ƙasar Guinea ya gana da friministansa

Sugaban ƙasar Guinea ya gana da friministansa da sojoji ke tsare da shi a gidansa

default

Sojojin ƙasar Guinea Bisau

Sojoji da ke yin borai a ƙasar Guinea Bisau na ci gaba da tsare friministan ƙasar Carlos gomes junior a gidansa inda ake tsare da shi,to sai dai a yau kanfanin dilanci labarai na Faransa ya ambato cewa shugaban ƙasar na Guinea Malam Bacai Sanha ya gana da friministan nasa wanda suka yi shwarwari tare.Rahoton ya nuna cewa babban alƙali mai shigare da ƙara na kasar ta Guinea Amine Michel saad shine ya zo ya ɗauƙi friministan a gidansa tare da rakiyar sojojin suka isa har a fadar shugaban ƙasar.Tun da farko dai a wani taron gaugawa da majalisar ministocin ta kira a yau ta yi allah dai da abinda ta kira mayar da hannu a gogo baya na taka dokokin ƙasar da sojojin suka yi.Ko da shike haryanzu sojojin basu fito ba fili suka bayyana cewa juyin mulki ne ba sanan kuma babu wata kafar da ta bayyana haka ba, to amma masu lura da al amuran yau da gobe na hasashen yunƙurin sojojin ya saka ƙasar cikin ruɗani ..

Mawallafi :Abdourahamane Hassane

Edita : Abdullahi Tanko Bala