Shugaban ƙasar Ekwado ya ƙetara rijiya da baya | Labarai | DW | 01.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban ƙasar Ekwado ya ƙetara rijiya da baya

Sojoji masu biyayya ga gwamnati sun maida shugaban Ekwado Rafael Korrea kan karagar mulki

default

Shugaban Ekwado Rafael Korrea

Shugaban ƙasar Ekwado Rafael Korrea ya ƙetara rijiya da baya, a yunƙurin juyin mulkin da ya fuskanta jiya daga`yan sanda tare da haɗin gwiwar wasu kuraten sojoji.

Shugaban ya samu mafaka a asibitin Quito babban birnin ƙasar. Ƙasashen duniya wanda suka haɗa da Amurika, Brazil, da ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai sun yi Allah wadai ga yunƙurin juyin mulkin. To sai dai rahotannin da suka hito daga fadar gwamnati a birnin Quito, sun ce sojoji masu biyayya ga shugaban ƙasa sun murƙushe juyin mulkin, kuma shugaban ya koma fadarsa.

A jawabin da ya yiwa al´umar ƙasa jim kaɗan bayan ya koma kujerarsa, Korrea ya ce ´yan sandar sun buƙaci hallaka shi har lahira, sakamakon matakin da ya ɗauka na rage masu albashi. A halin da ake ciki dai yanzu, shugaban rundunar ´yan sanda ta ƙasa ya yi murabus daga muƙaminsa. Mawwalafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal