1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban ƙasar Turkiyya ya amince da sabuwar gwamnati

August 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuCm

Praministan ƙasar Turkiyya Rejep Tayeb Erdogan, ya gabatar da sabuwar gwamnatin da za shi jagoranta, ga shugaban ƙasa Abdullahi Gül.

Ba da wata wata ba, shugaban ya amince da wannan gwamnati.

Wannan sabuwar gwamnati ,da aka girka kwana ɗaya rak bayan zaɓen shugaban ƙasa ta ƙunshi ministoci 25, wanda su ka haɗa da tsafi, da kuma sabin shiga.

Ali Babacan, ministan tattalin arziki ya gaji Abdellah Gül, a matsayin ministan harakokin waje.

Sabuwar gwamnatin kamar wadda ta gabata, ta ƙunshi mace ɗaya tilo.

A yammacin yau sabuwar majalisar ministocin, ta yi zaman taron ta na farko.

Sai kuma sati mai zuwa, majalisar dokoki za ta kaɗa ƙuri´ar amincewa ko akasin haka da ita.