Shugaban ƙasar Haiti ya sanar da cewa za a gudanar da zaɓuɓukan gama gari
July 1, 2010Talla
Shugaban ƙasar Haiti Rene Preval ya bada sanarwa cewa za a gudanar da zaɓubukan gama gari a cikin watan November mai zuwa, bayan girgiza ƙasar da ta auku a ƙasar a cikin watannin da suka gabata wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu ɗari biyu da hamsin .
Zaben wanda ya haɗa da na shugaban ƙasa dakuma na yan majalisu,shugaban hukumar wucin gadi dake kula da shirya zaɓen Pierre Louis Opont ya shedda cewa za a kashe kuɗaɗe har miliyan 29 na dala Amurka.A yanzu dai gwamnatin ƙasar Haiti ta zuba milyan bakwai na dala Amurka sauran cikon kuɗaɗen kuwa zasu zone daga ƙasashen duniya.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umar Aliyu