1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Zuma ya yi watsi da murabus

February 14, 2018

Shugaban kasar Afirka ta Kudu ya ce ba zai yi murabus ba duk da shirye-shirye da ma kiraye-kirayen da ajiye aiki da ake yi a fadin kasar. Shugaban dai na fuskantar tsananin matsin lamba a yanzu.

https://p.dw.com/p/2sg5g
Südafrika Präsident Jacob Zuma
Shugaba Jacob Zuma na kasar Afirka ta KuduHoto: picture-alliance/dpa/AP/K. Mokone

Shugaba Jacob Zuma na kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi masa na ya yi murabus daga matsayinsa na shugaban kasa, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin adalci a gare shi.

Shugaba Zuma dai ya fadi haka ne dai dai kuma lokacin da Jam'iyyar ANC mai mulkin kasar ke tabbatar da cewa majalisar dokokin kasar za ta yanke masa kauna a gobe Alhamis inda nan take za a nada wanda zai maye gurbin shugaban kasar.

A cewar jam'iyyar ANC, za ma a tabbatar sabon shugaban kasar a goben, inda zai yi wa 'yan kasa jawabi ba tare da wani bata lokaci ba. Tun da fari dai a wannan Laraba, sai da 'yan sandan Afrika ta kudun suka mamaye yankunan da attajiran Gupta suke, attajiran da ke da alaka da shugaba Jacob Zuma.