1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Vietnam ya mutu

Abdul-raheem Hassan
September 21, 2018

Fadar gwamnatin Vietnam ta tabbatar da mutuwar Shugaban kasar Tran Dai Quang bayan fama da dogon jinya sakamakon rashin lafiya.

https://p.dw.com/p/35HST
Vietnam Tran Dai Quang, Präsident
Hoto: Reuters/Kham

An dau lokaci ana rade-raden tsananin rashin lafiyar da shugaban ke fama da shi, musamman tun bayan da aka shugaban na ziyartar likitoci a kasashen waje. Wasu 'yan kasar sun ce rabon da su ga shuganan tun shekarar 2017 loakcin da ya halarci liyafar cin abinci da tawagar kasar Chaina da suka ziyarci kasar.

A shekara ta 2016 ne marigayin ya dare karagar mulki, inda shugabannin manyan kasashen duniya kamar Donald Trump suka ziyarce shi kasar a zamaninsa. A yanzu mataimakiyarsa Dang Thi Ngoc Thinh za ta shugabanci kasar kamar yadda dokokin kasar suka tanada kamin majalisar dokoki ta zabi sabon shugaban kasa a watan gobe na Oktoba.