1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugaba Schröder ya yi kira ga ba da kaimi wajen shawo kan matsalolin da Kungiyar Hadin Kan Turai ke huskanta a halin yanzu.

A halin yanzu, Kungiyar Hadin Kan Turai ta sami kanta ne cikin wani mawuyacin hali, bayan zabukan raba gardamar da aka gudanar a kasashen Faransa da Netherlands, inda `yan „na ki “, suka fi samun rinjayi. Firamiyan kasar Luxembourg, Jean-Claude Juncker, wanda kasarsa ce ke jagorancin kungiyar a halin yanzu, yana nan yana ta kokarin ganawa da sauran shugabannin kasashen kungiyar, don samad da tsari na bai daya, na irin kamun ludayin da za su yi nan gaba.

Shugaban gwamnatin tarayyar Jamus , Gerhard Schröder(a hagu) da Firamiyan kasar Luxembourg, Jean-Claude Juncker, a ganawar da suka yi a birnin Luxembourg.

Shugaban gwamnatin tarayyar Jamus , Gerhard Schröder(a hagu) da Firamiyan kasar Luxembourg, Jean-Claude Juncker, a ganawar da suka yi a birnin Luxembourg.

Bayan kayen da Kungiyar Hadin Kan Turai ta sha, a zaben raba gardamar da aka gudanar a kasashen Luxembourg da Faransa, inda mafi yawan al’umman kasashen biyu, suka yi watsi da kundin tsarin mulkin kungiyar, yanzu tamabayar da ake yi ita ce, ina kuma aka nufa ?

Game da samo wani tsari na irin kamun ludayin da shugabannin kasashen kungiyar za su yi nan gaba ne, Firamiyan kasar Luxembourg, Jean-Claude Juncker, wanda a halin yanzu, kasarsa ce ke jan akalar harkokin kungiyar EUn, ya fara tattaunawa da takwarorinsa. A jiya ne dai shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Gerhard Schröder, ya kai masa ziyara a birnin Luxembourg, inda suka yi shawarwari kan cim ma daidaito game da tsarin kasafin kudin kungiyar. A cikin makwanni biyu masu zuwa ne duk shugabannin kasashen kungiyar za su yi taron koli, har ila yau dai a birnin na Luxembourg, don nemo bakin zaren warware matsalar da a halin yanzu ke barazanar janyo wargajewarta. A huskar kasafin kudin kungiyar dai, Jamus da sauran wasu kasashe 5, wadanda su ne suka fi ba da gudummuwa, sun dage kan matsayinsu na cewa, bai kamata gudummuwar da ko wace kasa za ta biya ta zarce kashi daya cikin dari na kudaden shigarta ba.

Amma bayan tattaunawar da ya yi da Firamiyan, na kasar Luxembourg, Jean-Claude Juncker, shugaba Schröder ya bayyana cewa:-

„Bai kamata a halin yanzu mu mai da batun kare maslahar kasashenmu tamkar abin da ya fi muhimmanci ba. Jamus dai a shirye take ta ba da tata cikakkiyar gudummuwa, iya gwargwado. Na bayyana wa shugaban haka, amma muna sa ran cewa, sauran kasashe ma za su bi wannan misalin.“

A kasar Luxembourg din dai, rahotanni sun ce Juncker ya gabatad da wata shawara, ta cim ma daidaito tsakanin kudaden gudummuwar da ake biya da kuma kasashen da za su fi samun taimako daga kungiyar. Amma duk haka, masu sukar lamiri na ganin cewa, shawarar ba za ta iya janyo sauyi ga ra’ayin da jama’a ke da shi game da kundin tsarin mulkin kungiyar ba.

Shugaba Schröder dai ya nuna goyon bayansa, ga yunkurin da Firamiyan na kasar Luxembourg din ke yi, wajen ceto kundin tsarin mulkin, da kuma ganin cewa sauran kasashe sun amince da shi. Sai dai ya yi kakkausar suka ga jam’iyyun adawar Jamus, wadanda a nasa ganin, ke yunkurin gindaya wa kungiyar wani sabon shinge, inda ya bayyana cewa:-

„Akwai hanyoyi biyu wajen tinkarar matsalar: daya ita ce yin amfani da halin da kungiyar ke ciki yanzu, wajen gurgunta kyakyawan yunkurin da ake yi na cim ma hadin kan Turai. Abin takaici ne, lura da cewa, jam’iyyun adawan Jamus na nuna alamar bin wannan hanyar. daya hanyar kuma, wadda na fi gwammace wa, ita ce dagewa wajen cim ma wannan gagarumin burin na hadin kan Turai, da kuma warware matsalolin da ake fama da su a halin yanzu.“

Shugaba Schröder na sukar `yan adawar ne saboda kiran da jam’iyyun, na CDU da CSU suka yi, na a dakatad da tattaunawar da aka shirya yi ta karbar kasar Turkiyya cikin kungiyar.

A birnin Brussels dai, ana tuntubar gabatad da wata shawara ne, wadda za ta bukaci shugabannin kasashen, da su zartad da wani kuduri, a taron kolinsu da za su yi a cikin makwanni biyu masu zuwa, na tsawaita wa’adin zartad da kundin da shekara daya, wato har zuwa shekara ta 2007, inda sauran kasashen za su sami lokacin yin tunani mai zurfi kan mamkomar kungiyar. Mai yiwuwa kafin wannan lokacin, a sake shirya wani zaben raba gardama kuma a kasashen Faransa da Netherlands.

 • Kwanan wata 03.06.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvbV
 • Kwanan wata 03.06.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvbV