Shugaba Putin ya sallami babban alkalin gwamnatin Rasha | Labarai | DW | 02.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Putin ya sallami babban alkalin gwamnatin Rasha

A wani mataki na bazata, shugaban Rasha Vladimir Putin ya sallami fitaccen babban alkalin gwamnatin kasar Vladimir Ustinov. Bisa umarnin shugaba Putin yanzu haka majalisar tarayyar ta dakatar da alkalin mai shekaru 53 daga aiki. Hukuma ta ce an sallami Ustinov din bisa son ranshi. To amma wata majiyar fadar Kremlin ta ce sallamar babban alkalin na daga cikin jerin matakan sake fasalta hukumomin kasar da shugaba Putin ke dauka. A ´yan kwanakin da suka wuce shugaban ya yi suka game da rashin samun nasara a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa.