Shugaba Putin ya fara wata ziyarar aiki a Japan | Labarai | DW | 20.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Putin ya fara wata ziyarar aiki a Japan

Shugaban Rasha Valdimir Putin ya isa birnin Tokyo a wata ziyarar aiki ta yini 3 a kasar Japan. A gobe litinin Putin zai tattauna da FM Japan Junichiro Koizumi. Sannan a ranar talata ya gana da sarkin sarakuna Akihito. Muhimmin batun da za´a mayar da hankali kai a tattaunawar da za´a yi da gwamnatin birnin Tokyo shi ne na fadada huldar cinikaiya sai kuma na takaddamar da kasashen biyu ke yi akan wasu tsibirai 4 dake cikin tekun Pasifik wadanda ko-wace daga cikin kasashen biyu ta ce mallakin ta ne. Tun a karshen yakin duniya na biyu tsohuwar daular tarayyar Sobiet ta mamaye wadannan tsibiran.