1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Putin ya ce bai kamata a yi amfani da karfi kan Iran ba

May 10, 2006
https://p.dw.com/p/Buys

Shugaban Rasha Vladimir Putin yayi amfani da jawabinsa na shekara shekara wajen yiwa Amirka gargadin cewa kada ta yi amfani da karfin soji akan Iran dangane da shirinta na nukiliya. A cikin jawabin wanda ya yi a fadar Kremlin, shugaba Putin ya ce ba a kullum ne amfani da karfi kai ga cimma sakamakon da ake bukata kana kuma matsalolin da wannan mataki kan haifar sukan fi barazanar da aka yi tsammani da farko. Putin ya kuma saka ayar tambaya game da sanya wa Iran takunkumi. A game da halin da Rashan ke ciki, shugaban ya yi tir game da matsalar cin hanci da rashawa da ta yiwa kasarsa katoto, kuma take kawo cikas wajen farfado da tattalin arzikin kasar ta Rasha. Putin ya kuma yi alkawarin cewa Rasha zata ci-gaba da biyawa abin da ya kira kawayenta na al´ada bukatunsu na makamashi.