1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Putin ya ba da shawarar warware rikicin iskar gas da Ukraine

December 31, 2005
https://p.dw.com/p/BvEI

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gabatar da wata shawara da nufin warware cece-kucen da ake yi dangane da sayarwa kasar Ukraine da iskar gas. Shugaba Putin ya ce idan Ukraine ta sanya hannu kan shirin tayin kafin karfe 12 dare na yau, to tana iya ci-gaba da biyan Rasha farashin da ta saba har zuwa karshen watan maris. Amma daga farkon watan afrilu dole ne Ukraine din ta saye iskar gas din akan karin farashin da kamfanin gas na Rasha wato Gasprom ya sanya, wato ninkin na yanzu har sau hudu. Da farko dai Rasha ta yi barazanar katse tura iskar gas din zuwa Ukraine daga gobe lahadi wato ranar daya ga watan janeru. Shugaban Ukraine Viktor Yushchenko mai ra´ayin ´yan yamma ya ce a shirye gwamnatinsa ta ke ta sasanta.