1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Prodi na kasar Italiya a Afghanistan

December 23, 2007
https://p.dw.com/p/CfY3

Shugaban ƙasar Italiya Romani Perodi, ya ziyarci Afhganistan a ƙarshen wannan mako, inda ya sadu da shugaba Hamid Karzai tare da babban kwamandan rundunar ISAF na ƙarkashin ƙungiyar NATO dake yaƙar dakarun Taliban. Majiyar ofishin jakadancin Italiya, tace shugaba Prodi, zai ziyarci jami’an tsaron Italiya da ke wanzar da tsaro a yanmacin kasar. Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da Prain-Ministan Australia Kevin Rudd, sune farko cikin shugabannin ƙasashen Turai da suka ziyarci Afghanistan a ‘yan makwannin baya-bayan nan, inda suke da jami’an tsaro cikin rundunar ISAF.