Shugaba Obasanjo ya kafa dokar tabaci a jihar Ekiti | Labarai | DW | 19.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Obasanjo ya kafa dokar tabaci a jihar Ekiti

Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya kafa dokar tabaci a jihar Ekiti mai fama da rikici dake kudu maso gabashin kasar. A ranar litinin majalisar dokokin jihar ta tsige gwamna Ayo fayose da mataimakiyarsa Biodun Olujimi bisa laifin cin hanci da rashawa. Daga bisani alkalin gwamnati ya nada kakakin majalisar Friday Aderemia mukamin gwamnan rikon kwarya. Duk da sukar wannan mataki da majalisar da dauka da cewa ya sabawa kundin tsarin mulki, sabon gwamnan ya dage kan sabon mukaminsa. Yanzu haka dai shugaba Obasanjo ya nada wani tsohon gwamnan sojin jihar Ogun da ya tafiyar da al´amuran jihar ta Ekiti kafin a tantance wanda ya cancanci darewa kan wannan kujera.