1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Nicolas Sarkozy ya gana da Shugaba Mahmud Abbas

September 27, 2010

Sarkozy ya ce ƙasashen Turai su taka rawan gani wajen wanzar da zaman lafiya a yankin gabas taskiya

https://p.dw.com/p/PO1W
Shugaba Nicholas Sarkozy da Shugaba Mahmud AbbasHoto: AP

Shugaban Fararansa Nicolas Sarkozy ya ce zai karɓi baƙuncin shugabanin Israela da na Palasɗinu a wata mai kamawa. Sarkozy ya bayyana haka ne a yayin da yake neman ƙasashen turai da ma ƙasashen da ke tekun Meditaranean da su taka rawan gani wajen samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Shugaba Sarkozy,|wanda a yau ya karɓi baƙuncin shugaba Mahmud Abbas na Palasɗinu, ya nemi ya san makomar tattaunawar samar da sulhu a yankin ta gabas ta tsakiya da aka riga aka fara, ya kuma buƙaci a sake ɗage wa'adin gine-ginen Israela da aƙalla watani ukku zuwa huɗu.

Daga bisani dai Sarkozy ya ce Abbas, da shugaban Israela Benjamin Netanyahu da shugaban Masar Hosni Mubarak za su ziyarci Paris a watan Oktoba domin yin shirin wani taron ƙoli na ƙasashen tekun Meditarenean da za'a gudanar a watan Nuwamba. Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Umaru Aliyu