1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Musharraf ya tabbtara da kashe Abu Hamza Rabia

Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan ya tabbatar da rahotannin da aka bayar cewa an kashe wani babban kwamandan kungiyar ´yan ta´adda ta Al-Qaida a wani yankin dake kusa da kan iyakar kasar da Afghanistan. Da farko wata jaridar Pakistan ta ce an kashe Abu Hamza Rabia kwamandan kungiyar al-Qaida. Jaridar ta ce Abu Hamza na daga cikin sojin sa kai 5 da aka kashe a arewacin yankin Waziristan a ranar alhamis da ta gabata. Jami´an leken asiri sun ce Abu Hamza wanda dan asalin kasar Masar ne, shi ke kula da harkokin ketare na shugaban Al-Qaida osma Bin Laden.