Shugaba Musharraf ya kare hukumar leƙen asirin ƙasarsa daga zargin da ake yi mata na tallafa wa ’yan Talliban. | Labarai | DW | 01.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Musharraf ya kare hukumar leƙen asirin ƙasarsa daga zargin da ake yi mata na tallafa wa ’yan Talliban.

Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan, ya ce hukumar leƙen asirin ƙasarsa ba ta da hannu wajen farfaɗo da ƙungiyar Taliban a Afghanistan. Amma ya kuma ce mai yiwuwa tsoffin jami’an hukumar, waɗanda suka yi ritaya, suna ba ’yan Taliban ɗin taimako. Ya ce dai ana gudanad da bincike don gano gaskiyar lamarin.

Shugaban ya kuma bayyana damuwarsa ga rashin fahimtar masu sa ido daga Yamma, game da yadda ababa ke wakana a yankin. Su dai ’yan Taliban ɗin na iza wuta ne a yaƙin da suke yi da dakarun ƙasa da ƙasa da ke girke a Afghanistan ɗin. Sun dai sha kai farmaki kan dakarun inda suka halaka da yawa daga cikinsu.