1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Musharraf ya ce ba zai tattauna da masu kishin Islama ba

Shugaban Pakistan janar Pervez Musharraf ya kawad da yiwuwar sasantawa da masu kishin Islama da aka yiwa kawanya a cikin wani masallaci dake birnin Islamabad. Shugaba Musharraf ya fadawa shugabannin masallacin da su gaggauta sakin mata da kananan yara ko kuma su fuskanci abin da ya kira mutuwa. Ministan cikin gidan Pakistan Aftab Ahmed Shepao ya karfafa gargadin da shugaba Musharraf yayiwa masu kishin Islama dake cikin masallacin na Red Mosque.

“Wannan gargadi ne da ya zama wajibi su yi aiki da shi idan ba haka ba halin da ake ciki ka iya sauyawa. Suna yi garkuwa da dalibai maza da mata kuma suna son su yi amfani da su a matsayin garkuwar dan Adam.”

Tun a ranar talata da ta gabata daruruwan dakarun gwamnati a cikin motoci masu sulke suka yiwa masallacin kawanya.