Shugaba Musharraf ya ce ana iya kashe ´yan kishin Islama da suka ki ficewa daga masallacin Islamabad | Labarai | DW | 07.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Musharraf ya ce ana iya kashe ´yan kishin Islama da suka ki ficewa daga masallacin Islamabad

Shugaban Pakistan Pervez Musharraf ya yi kashedin cewa ana iya halaka ´yan kishin islama da ke cikin wani masallaci a birnin Islamabad idan ba su yi saranda ba. To sai dai babban limamin masallacin na Red Mosque ya ce da shi da magoya bayan sa na da tarin makamai da kayan abinci da zasu ishesu har nan da wata daya. Ya kuma kara da cewa dalibai kimanin 70 ciki har da mata 30 aka kashe sakamakon kawanyar da dakarun gwamnati ke yiwa masallacin tun a ranar talata da ta gabata. To sai dai alkalumman da gwamnati ta bayar na nuni da cewa mutane 19 ne suka mutu a wannan fito na fito.