Shugaba Muhammar Ƙaddafi ya cika shekaru 40 kan karagar mulki | Siyasa | DW | 01.09.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugaba Muhammar Ƙaddafi ya cika shekaru 40 kan karagar mulki

Waiwaye adon tafiya na shekaru 40 da shugaban ƙasar Libiya Mouhammar Ƙaddafi ya hau karagar mulki.

default

Ƙaddafi ya cika shekaru 40 kan kujerar mulkin Libiya

Yau ne shugaban ƙasar Libiya Muhammar Ƙaddafi ke cika shekaru 40 daidai da hawa karagar mulki.

An haifi shugaba Ƙaddafi a shekara ta 1942.

Yana ɗan shekaru 27 a duniya ya hamɓarar da Sarki Idriss, ranar ɗaya ga watan Satumba na shekara ta 1969.

Tun daga wannan lokaci, Kalan Ƙaddafi ke cigaba da jagorantar ƙasar Libiya, tare da sa toka sa katsi da manyan ƙasashen duniya.

Bayan kifar da sarautar gargajiya ya Ƙaddamar da Jamhuriya inda ya alƙawarta cewar Libiya zata kasance tarmamuwa sha kallo a duniya ta fannin cigaba, sannan , tare da ƙalubalantar ƙasashen yammancin duniya:Yace muna ɗaukar kanmu a matsayin garkuwa ga ƙasashe masu tasowa.Za mu gudanar da gwagwarmaya bil haƙi da gaskiya da turawan mulkin mallaka, dake ma´amilar kashin dankali da ƙasashe masu tasowa ta hanyar danne masu haƙƙoƙinsu.

ƘasashenTurai da Amurika na zargin Shugaba Muhhamar Ƙaddafi da yin amfani da maggudan kuɗaɗen da Libiya ke samu ta hanyar cinikayar man fetur wajen tallafawa ƙungiyoyion tawaye da na ´yan ta´ada, ko kuma wasu Ƙungiyoyi masu fafatakar neman ´yancin kamar su PLO a a Palestinu, ANC a Afrika ta Kudu kokuma yan ƙungiyar sandinistiya a Nikaraguwa.

A farkon shekarun 1980 ne aka shiga gadan gadan kafar wando guda, tsakanin Amurika da Libiya bayan da Amurika ta zargi wasu Libiyawa da kai hari a cikinwani gidan rawa na birnin Berlin inda sojojin Amurika biyu suka rasa rayuka.

Kwanaki kaɗan, sojojin Amurika suka maida martani ta hanyar ruwan bama bamai a a gidajen Ƙadafi dake Tripoli da Bengazi to amma shugaban ya ƙetara rijiya da baya.

To saidai a wani mataki na ana magani kai na ƙaba Libiya ta kitsa hare hare kan jiragen sama na Pan Am a sararrin samaniyar Lockerbie a Scotland, da wani jirgi samfarin UTA a sararin samaniyar Sahara.Daga nan Libiya ta kasance cikin takunkumi komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya.

A farkon shekarun 2000 shugaba Mohamed Kaddafi ya fara daidata muá lar Libiya da sauran ƙasashen duniya.

Matakin farko shine yin watsi da shirin mallakar makaman nukiliya abinda Firaministan Britaniya na wacen lokaci Tony Blair yayi lale marhabin da shi: Wannan shawara da Ƙaddfi ya yanke abun fari ciki ne, kuma mun yi lale marhabin da ita.

Sannu a hankali dai Libiya ta fara komawa sabuwar ma´amila da ƙasashen yammacin duniya.

A sakamakon hakan,Majalisar Ɗinkin Duniya ta cire takunkumin da ta ƙargama mata , sannan shekaru ukku da suka wuce, Amurika ta cire Libiya daga sahun ƙasashe masu ɗaurewa ta´adanci gindin a duniya.

Bikin na cikwan shekaru 40 yayi daidai da lokacin da Ƙaddafi ke jagorantar Ƙungiyar Tarayar Afrika, sannan a karon farko, cikin shekaru 40,a wannan wata na Satumba, zai halarci taron shugabanin ƙasashen Majalisar Duniya a Amurika.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Umaru Aliyu