1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Mahama na Ghana ya yi alkawarin hade kan 'yan kasa

January 7, 2013

Bayan ranstuwar kama aiki a wani biki a birnin Accra wanda babbar jam'iyar adawa ta kaurace masa, shugaban Ghana John Mahama ya ce zai cika alkawuran da ya dauka.

https://p.dw.com/p/17FaG
Hoto: Getty Images /AFP

A kalamunsa lokacin rantsuwar shugaban Ghana John Dramani Mahama ya ce a matsayin 'yan Ghana kamata yayi su gyara kasarsu da kansu kuma ba lalle ne sai sun dogara kan kasashen ketare ba kuma ko shakka babu kasar Ghana ta sami ci gaba sosai hakazalika ba a ce ba ta fuskanci matsaloli ba.

"Ina mai tabbatar muku cewar duk alkawuran da na dauka lokacin yakin neman zabe zan cika su."

Gabanin dai rantsar da shi sai da aka rantsar da mataimakinsa Kwesi Amissah Arthur.

Shugabanni da dama sun halarci bikin

Bikin dai ya samu halartar sama da kashi 70 cikin 100 na shugabanin kasashen yammacin Afrika da ma na wasu kasashen nahiyar Afirka kamar shugaba Kikweteh na kasar Tanzaniya da shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu.
Bikin ransuwar na wannan karo dai ya dauki wani sabon salo idan aka kwatanta da wadanda suka gabata domin an zuba jami'an tsaro da dama tare kuma da binciken jama'a sosai gabanin shiga dandalin Independence Square, a dayan hannu kuma aka hana wasu jama'a shiga harabar.

Ko da shi ke shugabanin kasar da suka gabata sun halarci bikin ciki har da tsohon shugaba John Kufuor na babbar jam'iyyar adawa ta NPP amma babu ko daya daga masu mara wa dan takarar jam'iyyar ta NPP wato Nana Akuffo Addo da ya halarci biki. Na dai nemi jin ta bakin Mr. Fred Oware farkon mataimakin shugabanr jam'iyyar ko mene ne dalilin haka.

John Dramani Mahama Präsident Amtseinführung Ghana
Hoto: Getty Images /AFP

"Ba mu da matsala da rantsarwar amma matsalarmu ita ce wanda ake rantsar da shi domin a ganin mu bA shi ne yayi nasarar zaben ba."
Tuni dai shugaban tarayyar Afirka kuma kuma shugaban kasar Benin Thomas Yayi Boni ya taya kasar Ghana murna.
"Madadin kasashen mambobi da ma jamhuriyar Benin muna taya ku murna ga irin rawar da kuka taka ya zuwa wannan lokkacin kuma Allah Ya taya shugaba Mahama riko ya kuma ba shi kwazo da himma na tafiyar da kasar."
Idan dai ba manta wata daya kacal kenan da Ghana ta gudanar da zabe amma madugun 'yan adawa ya ki ya amincewa da sakamakon zaben.

Mawallafiya: Rahmatu Abubakar Jawando
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani