Shugaba Maduro ya nemi sassaucin rikicin siyasa | Labarai | DW | 01.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Maduro ya nemi sassaucin rikicin siyasa

A jiya Juma'a dai a Banizuwela dakarun tsaro na kasar sun tarwatsa gangaminn dalibai ta hanyar baza su da harba hayaki mai sa hawaye saboda adawa da janye karfin ikon majalisar da 'yan adawa suka mamayeta.

Shugaban kasar Banizuwela Nicolas Maduro da sanyin safiyar Asabar din nan ya yi kira ga kotun kolin kasar ta sake nazari kan matakin da ta dauka na rage karfin iko na 'yan majalisa, matakin da ya janyo kakkausar suka daga bangaren adawa da ma gwamnatocin kasashen waje.

Wannan sanarwa dai na zuwa ne sa'oi kafin babban gangami da 'yan adawa da masu zanga-zanga suka shirya a wannan Asabar domin tofin alatsine da matakin na kotun koli. Bayan taron da aka yi cikin daren Juma'a da Shugaba Moduro ya jagoranta, babban kwamitin tsaro a kasar ya bayyana goyon bayan kotun ta sake nazari kan wancan mataki domin dorewar zaman lafiya a kasar.

A jiya Juma'a dai dakarun tsaro na kasar sun tarwatsa gangaminn dalibai ta hanyar baza su da harba hayaki mai sa hawaye saboda adawa da janye karfin ikon majalisar da 'yan adawa suka mamayeta tun zaben da aka yi a karshen shekarar 2015. 'Yan adawar dai na kallon matakin a matsayin juyin mulki da gwamnatin Moduro ta yi wa 'yan adawa cikin hikima.