Shugaba Lansana Konte yayi garambawul ga rundunar soja ta kasa | Labarai | DW | 10.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Lansana Konte yayi garambawul ga rundunar soja ta kasa

Shugaban kasar Guinee Konakry, Lansana Konte ya gudanar da wani gagaramin garambawul ga rundunar soja ta kasa.

Baki daya, sojoji 1.800 ne ya sallama daga bakin ayyuka.

Wata majiyar soja ta ambato cewa, shugaban ya dauki wannan mataki, domin tsabtace rundunonin da a ke zargi wasu daga sojojin da tsageranci, da kuma rashin biyyaya .

Sojojin da a ka sallama sun hada da Janar Mamadu Diallo shugaban rundunar sojojin kasa, da kuma tsofan ministan tsaro na kasar Guinee.

To saidai, masu lura da al´ammura a kasar na hasashen cewa, wannan garambawul, kan iya zama matsayin allura ta tono galma, ta hanyar tada rikicin tawaye.