Shugaba Kufour ya yi kira da a warware rikicin Guinea | Labarai | DW | 15.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Kufour ya yi kira da a warware rikicin Guinea

Anyi kira ga Guinea data gaggauta shawo kann matsalolin siyasa da kasar ke fama dasu ,domin kare rinchabewan lamura.Shugaban kungiyar gamayyar Afrika kuma shugaban kasar Ghana John Kufor ,wanda yayi wannan kiran ya kuma bayyana cewa a shirye kungiyar tarayyar Afrikan take wajen taimakawa kawo karshen wannan takaddama.Mr Kufour yace ya zamanto wajibi a mike tsaye wajen gano bakin zaren rigingimun dake haddasa cigaban asarar rayuka a yankuna dake fama da rigingimu a Afrika.