Shugaba Koriya Ta Kudu Roh ya fara ziyararsa ta biyu a Koriya Ta Kudu | Labarai | DW | 02.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Koriya Ta Kudu Roh ya fara ziyararsa ta biyu a Koriya Ta Kudu

Shugaban kasar KTK Roh Moo-Hyun ya isa a kasar KTA don gudanar da wani taron koli na kwanaki 3 da shugaban KTA Kim Jong-Il. Shugaba Roh ya tsallake kan iyakar kasashen biyu da kafa a wata alama ta sasantawa a wannan ziyara wadda ta ita ce ta biyu tun bayan shekara ta 2000. Daga bisani shugaba Kim Jong-Il ya tarbi takwaransa na KTK a birnin Pyongyang. An shirya taron kolin sakamakon ci-gaba da ake samu a tattaunawar nan ta kasashe 6 dake gudana a birnin Beijing da nufin lalata shirin nukiliyar KTA. A ranar lahadi mahalarta taron sun amince da wata yarjejeniyar wucin gadi akan mataki na gaba na kawo karshen shirin kera makaman nukiliyar KTA.