Shugaba Kibaki yayi kira ga makiyayya da su kwantar da hankali | Labarai | DW | 10.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Kibaki yayi kira ga makiyayya da su kwantar da hankali

Shugaban Kenya Mwai Kibaki yayi kira ga makiyaya a yankunan kasar dake fama da masifar fari da su guji fada da juna sakamakon kamfar ruwan da ake fama da ita yayin da halin da ake ciki a gabashin Afirka ke ta´azzara. A halin da ake ciki miliyoyin mutane da rayuwarsu ta dogara akan dabbobi a kasashen Kenya da Somalia da kuma Habasha sun shiga cikin wani mawuyacin hali sakamakon mutuwar dubban shanu, awaki da kuma rakumma a yankin. Shugaba Kibaki ya yi kira ga ´yan Kenya da su guji duk wani rikici da ka iya tasowa sakamakon kamfar ruwa, sannan ya ce gwamnati zata yi duk iya kokarin ganin kowa ya samu ruwan sha iya gwagwardo. A halin da ake ciki kasashen duniya na ci-gaba da yin gargadi game da aukuwar wata matsananciyar yunwa a yankin na gabashin Afirka.