Shugaba Kibaki ya amince da sakamakon zabe na raba gardama | Labarai | DW | 22.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Kibaki ya amince da sakamakon zabe na raba gardama

Alummar kasar Kenya sun yi watsi da sabon kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar jefa kuriar rashin amincewa a zaben raba gardama da aka gudanar a jiya litinin.

A cewar bayanai da suka iso mana daga kasar Tuni shugaban kasar wmai Kibaki ya amince da wannan sakamako ba tare da an kai ruwa rana ba.

Bugu da kari shugaba Kibaki ya kuma godewa Alummar kasar da suka fito don bayyana raayin su game da wannan mataki da gwamnatin ta dauka .

Watsi da sabon kundin tsarin mulkin a cewar Kibaki ba zai jefa kasar cikin rudani ba , tun da yake akwai tsohon kundin wanda za a ci gaba da amfani dashi.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa wannan zabe ya kasance irin sa na farko a tun lokacin da kasar ta samu yancin kanta daga turawan mulkin mallaka na Biritaniya a shekara ta 1963.